1 Samuel 25:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ki yi nazari a kai, ki ga ko za ki iya yin wani abu, domin masifa yana nan rataye a wuyan maigidanmu da dukan iyalin gidansa. Shi mugun mutum ne wanda ba wani da zai iya yin masa magana.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، سَيْ كِيِ تُنَانِ دَݣَوْ، كِيِ وَنِ أَبُ غَمٜىٰدَ ذَنْثٜىٰنَّنْ؞ وَنَّنْ يَجَٰوُاْوَ مَيْغِدَنْمُ دَ دُكَنْ غِدَنْسَ بَبَّرْ وَهَلَ؞ شِے وَنِ طَنْ إِسْكَ نٜىٰ دَ مُتُمْ بَذَيْ عِيَيِمَسَ مَغَنَبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu sai ki yi tunani, ki san abin da ya kamata ki yi, gama ana niyyar yi wa maigida da dukan gidansa ɓarna. Ga shi, maigida yana da mugun hali, ba zai ji kowa ba!”