1 Samuel 25:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبِغِيٜىٰلْ تَيِ سَوْرِ، تَ طَوْكِ دُنْڧُلٜىٰنْ غُرَاسَ طَرِے بِيُ دَ سَلْكُنَ بِيُ ثِكٜىٰ دَ ضُوً إِنَبِے دَ تُمَكِ بِيَرْ دَ عَكَ دَڢَ دَ غَسَشّٜىٰنْ حَڟِ مُودُ غُواْمَشَا عُكُ دَ ڧُنْشِنْ یَیَنْ إِنَبِے غُدَا طَرِے دَ دُنْڧُلٜىٰنْ ٻَوْرٜىٰ غُدَا طَرِے بِيُ، تَيِ لُواْدِنْسُ عَكَنْ جَاكُنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Abigail ta yi sauri, ta ɗauki malmalar abinci guda metan, da salkar ruwan inabi biyu, da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu uku, da nonnan 'ya'yan inabi guda ɗari, da kauɗar ɓaure guda metan, ta labta wa jakai.