1 Samuel 25:36 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبِغِيٜىٰلْ تَكُواْمَ تَسَامِ نَبَلْ أَغِدَا يَنَ بِكِ إِرِنْ نَسَرَاكُنَ؞ يَنَجِوَ رَنْسَ دَاطِے، يَكُمَ بُغُ تِلِسْ؞ دُواْمِنْ حَكَ بَتَثٜىٰ مَسَ كُواْمٜىٰبَ سَيْ وَشٜىٰغَرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Abigail ta koma wurin Nabal, ta iske shi yana biki irin na sarakuna a gidansa. Ya yi ta nishaɗi, ya bugu sosai, don haka ba ta ce masa kome ba sai da safe.