1 Samuel 26:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Dawuda ya ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da Shawulu suka tafi. Ba wanda ya gan su, ba wanda ya san abin da ya faru, ba kuwa wanda ya farka, dukansu suna barci gama Ubangiji ya sa barci mai nauyi ya ɗauke su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ دَاوُدَ يَطَوْكِ مَاشِ دَ غُواْرَنْ ضُوً دَسُكٜىٰ كُسَدَ كَنْ سَرْكِے، سَيْ سُكَ كُواْمَ؞ بَاوَنْدَ يَغَنْسُ، بَاوَنْدَ يَسَنْ أَبِنْدَ يَڢَرُ، بَا كُوَ وَنْدَ يَڢَرْكَ؞ دُكَنْسُ بَرْثِ مَيْ نَوْيِ دَغَ يَهْوٜىٰهْ يَكَامَسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da haka Dawuda ya ɗauki mashi da butar ruwan da yake wajen kan Saul, suka tafi. Ba wanda ya gansu, ba wanda ya sani, ba kuwa wanda ya farka, gama dukansu suna barci, domin Ubangiji ne ya sa barci mai nauyi ya share su.