1 Samuel 26:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya ce wa Abner, “Wane irin mutum ne kai? Ba kai ne soja mafi iya yaƙi a Isra’ila ba? Don me ba ka yi gadin ranka yă daɗe, sarki da kyau ba? Ɗazu wani ya shiga tsakiyarku don yă kashe ranka yă daɗe, sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ يَثٜىٰ «أَبْنٜىٰرْ، وَنٜىٰ إِرِنْ مُتُمْنٜىٰ كَيْ؟ بَكَيْنٜىٰ سُواْجَ مَڢِيَ عِيَ يَاڧِ عَ إِسْرَٰٓءِيلَ بَ؟ دُوانْمٜىٰ بَكَيِ غَادِنْ مَيْغِدَنْكَ سَرْكِے دَ ݣَوْبَ؟ طَظُ وَنِ يَشِغَ ڟَكِيَرْكُ دُواْمِنْ يَكَشٜىٰ مَيْغِدَنْكَ سَرْكِے!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda ya ce wa Abner, “Kai ba namiji bane? Wa yake kama da kai cikin Isra'ila? Me ya sa ba ka lura da mai girma, sarki ba? Wani mutum ya zo don ya hallaka mai girma sarki.