1 Samuel 26:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ دَ أَبِشَيْ سُكَ شِغَ سَنْسَنِنْ طَالُوتَ دَ دَرٜىٰ، سُكَ سَامٜىٰشِ يَنَ ݣُونْثِيَ أَڟَكِيَرْ سُواْجُواْجِ دَ مَاشِنْسَ عَكَڢٜىٰ عَڧَسَا كُسَدَ كَنْسَ؞ أَبْنٜىٰرْ دَ سَوْرَنْ سُواْجُواْجِنْ سُنَ بَرْثِ كٜىٰوَيٜىٰ دَشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Dawuda da Abishai, suka tafi sansanin Saul da dare. Suka tarar da Saul yana barci cikin sansani da mashinsa a kafe a ƙasa, wajen kansa. Abner kuwa da sauran sojoji suna kwance kewaye da shi.