1 Samuel 26:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبِشَيْ يَثٜىٰ وَ دَاوُدَ «يَوْ اللَّهْ يَبَادَ أَبُواْكِنْ غَابَنْكَ أَ حَنُّنْكَ؞ بَرِ إِنْ كَڢٜىٰشِ عَڧَسَا دَ مَاشِنَ، ذَنْ سُواْكٜىٰشِ دَ مَاشِ سَوْ طَيَ تَكْ، بَانَ بُڧَاتَ إِنْ سُواْكٜىٰشِ سَوْ بِيُ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka bar ni in nashe shi da mashi sau ɗaya kaɗai, in sha zararsa, in haɗa shi da ƙasa!”