1 Samuel 27:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Wata rana Shawulu zai kashe ni, abu mafi kyau da zan yi shi ne in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Da haka Shawulu zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra’ila, a can kuwa zan tsira daga hannunsa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَيِ تُنَانِ أَ رَنْسَ يَثٜىٰ «بَاشَكَّ وَتَرَانَ ذَنْ مُتُ أَ حَنُّنْ طَالُوتَ؞ بَا أَبِنْدَ ذَنْعِيَيِ سَيْ إِنْ غُدُ ذُوَا ڧَسَرْ ڢِلِسْتِيَاوَا؞ طَالُوتَ ذَيْ بَرْ نٜىٰمَنَ عَيَنْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، نِے كُمَ إِنْ كُٻُثٜىٰ دَغَ حَنُّنْسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda ya yi tunani a ransa, ya ce, “Wata rana Saul zai kashi ni, don haka ba abin da ya fi mini, sai in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Sa'an nan Saul zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra'ila. Zan kuwa tsira daga hannunsa.”