1 Samuel 27:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk lokacin da ya yaƙi wani wuri, ba ya barin namiji ko mace da rai, amma sai ya kwashe tumaki, da shanu, da jakuna, da raƙuma, da riguna, sa’an nan yă koma wurin Akish.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ سَعَدَّ دَاوُدَ يَڢَاطَ مُسُ دَ يَاڧِ، بَايَ بَرِنْ نَمِجِ كُواْ مَثٜىٰ دَ رَيْ؞ يَكَنْ ݣُوشِ أَوَكِ دَ شَانُو دَ جَاكُنَ دَ رَاڧُمَ دَ رِيغُنَ؞ سَعَنً يَكُواْمَ وُرِنْ عَكِشْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda yakan fāɗa wa ƙasar, ya hallaka ta, ba zai bar mace ko namiji da rai ba. Ya kuma kwashe tumaki, da shanu, da jakai, da raƙuma, da tufafi, ya komo zuwa wurin Akish.