1 Samuel 29:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Komandodin Filistiyawa suka ce, “Waɗannan Ibraniyawa kuma fa?” Akish ya ce, “Wannan shi ne Dawuda hafsan Shawulu, sarkin Isra’ila. Yana nan tare da ni shekara guda ke nan. Ban kuwa taɓa samunsa da wani lahani ba tun daga ranar da ya bar Shawulu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَنْيَنْ سُواْجُواْجِنْ ڢِلِسْتِيَ سُكَ تَمْبَيِ عَكِشْ سُكَثٜىٰ «مٜىٰنٜىٰنٜىٰ إِبْرَنِيَاوَنَّنْ سُكٜىٰيِ أَنَنْ؟» عَكِشْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «وَنَّنْ دَاوُدَ نٜىٰ وَنْدَ يَيِ وَ طَالُوتَ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ حِدِمَ؞ يَڢِ شٜىٰكَرَا طَيَ تَرٜىٰدَنِ؞ كُمَ تُنْدَغَ رَانَرْدَ يَبَرْ طَالُوتَ يَذُواْ وُرِينَ بَنْ تَٻَ سَامُنْسَ دَ لَيْڢِے بَ كُواْ كَطَنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shugabannin sojojin Filistiyawa suka ce, “Me waɗannan Ibraniyawa suke yi a nan?” Akish kuwa ya ce wa shugabannin sojojin Filistiyawa, “Ai, wannan Dawuda ne baran Saul, Sarkin Isra'ila, wanda yake tare da ni tun da daɗewa. Tun lokacin da ya zo wurina ban taɓa samunsa da wani laifi ba.”