1 Samuel 29:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma komandodin Filistiyawa suka yi fushi, suka ce, “Ka sa mutumin nan yă koma zuwa wurin da ka ba shi yă zauna. Ba zai bi mu zuwa wurin yaƙi ba. Yana iya juya a kanmu lokacin yaƙin. Zai iya yin amfani da wannan zarafi yă ciccire kawunanmu don yă faranta wa maigidansa rai?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا مَنْيَنْ سُواْجُواْجِنْ ڢِلِسْتِيَ سُكَيِ ڢُشِے دَ عَكِشْ، سُكَثٜىٰ مَسَ «كَسَا مُتُمِنَّنْ يَكُواْمَ ذُوَا وُرِنْدَ كَبَاشِ يَذَوْنَ؞ بَذَيْبِيمُ ذُوَا وُرِنْ يَاڧِنْ بَ؞ يَنَ عِيَ جُويَا عَكَنْمُ لُواْكَثِنْ يَاڧِنْ؞ ذَيْ عِيَيِنْ أَمْڢَانِ دَ وَنَّنْ ظَرَڢِ يَثِثِّرٜىٰ كَوُنَنْمُ دُواْمِنْ يَڢَرَنْتَوَ مَيْغِدَنْسَ رَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma shugabannin sojojin Filistiyawa suka husata da shi, suka ce masa, “Ka sa mutumin nan ya koma wurin da ka zaunar da shi. Ba zai tafi tare da mu zuwa wurin yaƙin ba, don kada ya juya mana gindin baka. Ai, da kawunan mutanenmu ne zai yi sulhu da ubangijinsa.