1 Samuel 29:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Akish ya kira Dawuda ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, na amince da kai tun daga ranar da ka zo wurina har yă zuwa yau, ban same ka da wani laifi ba, na kuma yi farin ciki in sa ka a cikin sojojina don ka yi mini aiki. Amma masu mulki nawa ba su yarda da kai ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عَكِشْ يَكِرَا دَاوُدَ يَثٜىٰمَسَ «نَا ضَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ، كَيْ مَيْ أَمِنْثِنٜىٰ، نَسُواْ كَتَڢِے كَيِ يَاڧِ تَرٜىٰدَ سُواْجُواْجِنَ؞ بَنْ تَٻَ سَامُنْكَ دَ لَيْڢِے بَ تُنْ رَانَرْدَ كَذُواْ وُرِينَ حَرْ ذُوَا يَنْذُ؞ عَمَّا سَوْرَنْ شُوغَبَنِّنْ بَسُ يَرْدَ دَكَيْبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akish kuwa ya kira Dawuda, ya ce masa, “Kai amintacce ne a ganina, daidai ne kuma ka tafi yaƙi tare da ni, gama ban same ka da wani laifi ba tun daga ranar zuwanka wurina har yau, duk da haka sarakunan ba su amince da kai ba.