1 Samuel 3:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya. Sai Sama’ila ya ce, “Yi magana gama bawanka yana saurara.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ كُوَ يَسَاكٜىٰ ذُوَا أَوُرِنْ يَڟَيَ يَيِ كِرَا يَثٜىٰ «سَمَٰعِيلَ! سَمَٰعِيلَ!» سَيْ سَمَٰعِيلَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «يِمَغَنَ غَمَا بَاوَنْكَ يَنَجِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuma ya zo ya tsaya, ya yi kira kamar dā, ya ce, “Sama'ila! Sama'ila!” Sama'ila ya amsa ya ce, “Ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.”