1 Samuel 30:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Wane ne ubangidanka, kuma daga ina ka fito?” Ya ce, “Ni mutumin Masar ne, bawan wani mutumin Amalek. Maigidana ya ƙyale ni sa’ad da na yi rashin lafiya kwanaki ukun da suka wuce.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَتَمْبَيٜىٰشِ يَثٜىٰ «وَنٜىٰنٜىٰ شُوغَبَنْكَ، كُمَ كَيْ دَغَ إِنَا نٜىٰ؟» سَيْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «نِے مُتُمِنْ ڧَسَرْ مَصَرْ نٜىٰ، بَاوَنْ وَنِ مُتُمِنْ أَمَلٜىٰكْ؞ ݣُونَكِے عُكُ دَ سُكَ وُثٜىٰ نٜىٰ شُوغَبَنَ يَڨَلٜىٰنِ أَنَنْ غَمَا إِنَ ثِيوُاْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda kuwa ya tambaye shi, “Wane ne ubangidanka? Daga ina ka fito?” Ya amsa, ya ce, “Ni saurayi ne, Bamasare, baran wani Ba'amaleke. Kwana uku ke nan da ubangidana ya tafi ya bar ni a baya saboda ba ni da lafiya.