1 Samuel 30:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bari a bakin Kwarin Besor, sai suka taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa’ad da Dawuda ya zo kusa da su, sai ya gaishe su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ يَكُواْمَ وُرِنْ مُتَنٜىٰ طَرِے بِيُنْ دَ بَسُ عِيَ بِنْسَبَ سَبُواْدَ يَوَنْ غَاجِيَ؞ سُونٜىٰ عَكَ بَرْسُ أَ رَاڢِنْ بٜىٰسُوارْ؞ سُكَتَاشِ سُكَ تَرْيِ دَاوُدَ دَ مُتَنٜىٰنْسَ؞ سَعَدَّ دَاوُدَ يَكَيْ كُسَدَسُو، سَيْ يَغَيْشٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bar su a rafin Besor, sai suka tafi su taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa'ad da Dawuda ya zo kusa da su ya gaishe su.