1 Samuel 4:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتُمِنَّنْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُنْ غُدُ أَغَبَنْ ڢِلِسْتِيَاوَا، كُمَ أَنْكَشٜىٰ سُواْجُواْجِ دَيَوَ؞ یَیَنْكَ هُواڢْنِ دَ ڢِنٜىٰهَسْ دُكَ سُنْ مُتُ، أَنْكُمَ ڨُوثٜىٰ عَݣُوتِ نَ اللَّهْ ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai wanda ya kawo labarin ya ce, “Isra'ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, an kashe mutane da yawa, har ma da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, sun rasu, an kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”