1 Samuel 5:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari da safe da mutanen Ashdod suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Sai suka ɗauki Dagon suka ajiye a wurin zamansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَشٜىٰغَرِ دَ سَسَّڢٜىٰ مُتَنٜىٰنْ أَشْدُوادْ سُكَتَاشِ سُكَ سَامِ دَغُوانْ يَڢَاطِ دَ ڢُسْكَ عَڧَسَا أَغَبَنْ عَݣُوتِ نَ يَهْوٜىٰهْ ؞ سُكَ طَغَ دَغُوانْ سُكَ مَيَرْ دَشِ عِنْدَ يَكٜىٰ أَدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kashegari da safe sa'ad da mutanen Ashdod suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Suka ta da shi, suka ajiye a wurinsa.