1 Samuel 5:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا وَشٜىٰغَرِ دَ سَسَّڢٜىٰ، سُكَسَاكٜىٰ سَامُنْ غُنْكِنْسُ دَغُوانْ يَڢَاطِ عَڧَسَا أَغَبَنْ عَݣُوتِ نَ يَهْوٜىٰهْ ؞ أَوَنَّنْ لُواْكَثِ، كَنْسَ دَ حَنُّوَنْسَ دُكْ سُنْ كَكَّرْيٜىٰ سُنَ ظُبٜىٰ عَبَاكِنْ ڧُواْڢَ، غَنْغَرْ جِكِنْ ثٜىٰ كَطَيْ تأَنَانً؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kashegari da safe kuma da suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Kan Dagon da hannuwansa a gutsure, suna nan a dokin ƙofa. Gangar jikin ce ta ragu.