1 Samuel 5:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka suka kira duka shugabannin Filistiyawa suka tambaye su, suka ce, “Me za mu da akwatin alkawarin Allahn Isra’ila?” Sai suka amsa suka ce, “A ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a kai shi Gat.” Sai suka ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ كِرَا دُكَنْ سَرَاكُنَنْ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَ تَمْبَيٜىٰسُ سُكَثٜىٰ «مٜىٰنٜىٰنٜىٰ ذَامُيِ دَ عَݣُوتِ نَ اللَّهْنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؟» سَرَاكُنَنْ سُكَ أَمْسَ مُسُ سُكَثٜىٰ «كُوُثٜىٰ دَ عَݣُوتِ نَ اللَّهْنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذُوَا بِرْنِنْ غَتْ»؞ سَيْ سُكَ طَوْكٜىٰشِ ذُوَا غَتْ، وَنِ بِرْنِنْ ڢِلِسْتِيَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka aika, aka kirawo dukan sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka ce musu, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila?” Suka ce, “Sai a kai shi Gat.” Su kuwa suka kai shi can.