1 Samuel 6:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Lawiyawa suka saukar da akwatin alkawarin Ubangiji tare da babban akwati mai siffofin zinariya na ɓeraye da marurai suka ajiye su a kan ƙaton dutse. A wannan rana mutanen Bet-Shemesh suka miƙa hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ لَوِيَاوَا سُكَ طَغَ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ نَ يَهْوٜىٰهْ تَرٜىٰدَ عَݣُوتِ مَيْ صِڢُّواْڢِنْ ظِينَارِيَ؞ سُكَ أَجِيٜىٰ عَݣُوتُنَنْ عَكَنْ ڧَتُوانْ دُوڟٜىٰنْ؞ سَيْ مُتَنٜىٰنْ بٜىٰتْ شٜىٰمٜىٰشْ سُكَ مِيڧَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا تَرٜىٰدَ وَطَنْسُ هَدَايُ غَ يَهْوٜىٰهْ أَ رَانَرْ نَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Lawiyawa kuwa suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji da akwatin da yake gefensa wanda aka sa siffofin zinariya a ciki. Suka ajiye su a kan babban dutsen. Mutanen Bet-shemesh kuwa suka miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu kuma a wannan rana.