1 Samuel 6:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Filistiyawa suka kira firistoci da bokaye suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku gaya mana yadda za mu komar da shi inda ya fito.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَ كِرَا تَارُوانْ ڢِرِسْتُواْثِنْ غُمَكَنْسُ تَرٜىٰدَ مَلَمً دُوبَا؞ سُكَ تَمْبَيٜىٰسُ سُكَثٜىٰ «مٜىٰنٜىٰنٜىٰ ذَامُيِ دَ عَݣُوتِ نَ يَهْوٜىٰهْ ؟ أَ ڢَطَا مَنَ تَيَيَا ذَامُ عَيْكَدَشِ ذُوَا وُرِنْدَ يَڢِتُواْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Filistiyawa suka kirawo firistocinsu da bokayensu, suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku sanar da mu yadda za mu komar da shi inda ya fito.”