1 Samuel 6:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Yanzu fa ku shirya sabon keken shanu da shanu biyu masu ba wa ’ya’yansu nono, waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba. Ku daure keken shanu wa shanun, amma ku tsare ’yan maruƙansu a gida.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَنْذُ سَيْ كُيِ سَابُوانْ كٜىٰكٜىٰنْ شَانُو، كُسَامِ شَانُو بِيُ مَاسُ بَا یَیَنْسُ نُواْنُواْ، كُمَ وَطَنْدَ بَعَتَٻَ رَاتَيَ مُسُ غُنْغُمٜىٰنْ وُيَنْ شَانُنْ نُواْمَبَ؞ كُطَوْرَ وَشَانُنْ كٜىٰكٜىٰنْ، عَمَّا كُطَوْرٜىٰ یَیَنْسُ أَغِدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu kuwa ku yi sabon keken shanu, ku sami shanun tatsa biyu waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba, ku ɗaura wa shanun keken, amma ku tsare 'yan maruƙansu a gida.