1 Samuel 6:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku ɗauki wani akwati ku sa siffofin zinariyan nan a ciki, waɗanda za su zama kyautai na shafen laifi, ku ajiye kusa da Akwati na UBANGIJI. Bayan haka sai ku sa keken shanun da akwatin a hanya, ku bar shi yă tafi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُطَوْكِ وَنِ عَݣُوتِ كُسَا صِڢُّواْڢِنْ ظِينَارِيَرْ نَنْ عَثِكِ، وَطَنْدَ ذَاسُ ذَمَ ݣَوْتَيْ نَشَاڢٜىٰ لَيْڢِے، كُ أَجِيٜىٰ كُسَدَ عَݣُوتِ نَ يَهْوٜىٰهْ ؞ بَايَنْ حَكَ سَيْ كُسَا كٜىٰكٜىٰنْ شَانُنْ دَ عَݣُوتِنْ أَ حَنْيَ، كُبَرْسُ سُتَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ku sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken shanun, ku kuma sa siffofin maruran da na ɓerayen a cikin wani akwati ku ajiye a gefen akwatin alkawarin. Ku aika da waɗannan abubuwa tare da shi don yin hadaya ta laifi. Sa'an nan ku sa shi a hanya, a bar shi, ya tafi.