1 Samuel 8:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ تِلَسْتَ وَطَنْسُ سُذَمَ شُوغَبَنِّ عَكَنْ سُواْجُواْجِ دُبُو دُبُو دَ سُواْجُواْجِ حَمْسِنْ حَمْسِنْ؞ یَیَنْكُ مَظَا ذَاسُ نُواْمٜىٰ غُواْنَكِنْسَ، سُغِرْبٜىٰ حَڟِنْسَ، سُڧٜىٰرَ مَسَ كَايَنْ يَاڧِنْسَ دَ نَكٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. 'Ya'yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa.