1 Samuel 8:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ مَسَ «كَجِ بُڧَاتَرْسُ، كَنَطَ مُسُ سَرْكِے؞» سَيْ سَمَٰعِيلَ يَثٜىٰ وَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا «تُواْ، أَنْجِ، كُواْوَ يَكُواْمَ غَرِنْسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuwa ya ce wa Sama'ila, “Ka yarda da abin da suka ce, ka naɗa musu sarki.” Sai Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Kowa ya koma gida.”