1 Samuel 9:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mai dahuwan ya ɗauko cinya da abin da yake bisanta ya kawo ya ajiye a gaban Shawulu. Sama’ila ya ce, “Ga abin da aka ajiye dominka. Ka ci, gama an keɓe shi dominka saboda wannan hidima daga lokacin da na ce, ‘Na gayyaci baƙi.’ ” Shawulu kuwa ya ci tare da Sama’ila a ranan nan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَيْ دَڢَ عَبِنْثِ يَكَٰوُاْ سَاشٜىٰ مَڢِے ݣَوْ نَڧَڢَ يَأَجِيٜىٰوَ طَالُوتَ؞ سَيْ سَمَٰعِيلَ يَثٜىٰ مَسَ «وَنَّنْ نٜىٰ نَامَنْ دَ عَكَ أَجِيٜىٰ دُواْمِنْكَ؞ كَثِ، دُواْمِنْ نَكٜىٰٻٜىٰ مَكَ شِ دُواْمِنْ كَثِ أَوَنَّنْ لُواْكَثِ تَرٜىٰدَ بَڧِنْدَ نَغَيَّتَ؞» أَ رَانَرْ نَنْ كُوَ طَالُوتَ يَثِ تَرٜىٰدَ سَمَٰعِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai mai dahuwa ya kawo cinya da gadon baya ya ajiye a gaban Saul. Sa'an nan Sama'ila ya ce, “Sai ka ci naman da aka ajiye a gabanka, gama dominka aka ajiye shi don ka ci a wannan lokaci tare da waɗanda na gayyata.” A wannan rana kuwa Saul ya ci tare da Sama'ila.