1 Samuel 9:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma bawan ya amsa ya ce, “Duba, a wannan gari akwai wani mutumin Allah, ana ganin girmansa ƙwarai kuma duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa wataƙila zai gaya mana hanyar da za mu bi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَيْ مَعَيْكَثِنْ يَأَمْسَ مَسَ يَثٜىٰ «أَيْ، أَݣَويْ وَنِ مُتُمِنْ اللَّهْ أَغَرِنَّنْ وَنْدَ عَكٜىٰ بَاشِ غِرْمَ سُواْسَيْ، غَمَا دُكْ أَبِنْدَ يَڢَطَا يَكَنْ ثِكَ؞ مُتَڢِے وُرِنْسَ، وَتَڧِيلَ ذَيْ عِيَ ڢَطَا مَنَ عِنْدَ ذَامُبِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma baran ya ce masa, “Ai, akwai wani mutumin Allah a garin nan, ana kuwa ganin girmansa, domin duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa, watakila ya iya faɗa mana inda jakunanmu suke.”