1 Thessalonians 2:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama ku, ’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا كُو یَنْعُوَ، كُنْ ذَمَ مَاسُ كُواْيِ دَ دُكَنْ جَمَعَرْ مَاسُبِنْ اللَّهْ ثِكِنْ أَلْمَسِيحُ عِيسَىٰ ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ عَيَنْكِنْ يَهُودِيَ، غَمَا كُنْ شَا وَهَلَ دَغَ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْكُ، كَمَرْ يَدَّ سُكَشَا أَ حَنُّنْ يَهُودَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
'Yan'uwa, ku ne kuka zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da suke na Almasihu Yesu, waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, don ku ma kun sha wuya a hannun mutanen ƙasarku, kamar yadda ikilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,