1 Thessalonians 3:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَرِ يَڧَرْڢَڢَ ذُوثِيَارْكُ ثِكِنْ ڟَرْكِے، كُذَمَ مَرَسَ لَيْڢِے أَغَبَنْ اللَّهْ وَنْدَ يَكٜىٰ عُبَنْمُ، أَ رَانَرْ دَ عُبَنْغِجِنْمُ عِيسَىٰ ذَيْ دَاوُاْ تَرٜىٰدَ دُكَنْ ڟَرْكَكَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
har ya tsai da zukatanku ku zama marasa abin zargi cikin tsarki a gaban Allahnmu, Ubanmu, a ranar komowar Ubangijinmu Yesu, tare da dukan tsarkakansa.