2 Chronicles 1:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Solomon ya yi magana ga dukan Isra’ila, ga shugabannin mayaƙa dubu-dubu da shugabannin mayaƙa ɗari-ɗari, ga alƙalai da kuma ga dukan shugabanni a Isra’ila, kawunan iyalai,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُلَيْمَٰنُ كُوَ يَكِرَا دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ يَيِ مَغَنَ دَسُو، وَتُواْ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِ دُبُو دُبُو دَ نَطَرِے طَرِے دَ مَاسُ شَرِيعَ دَ دُكَنْ شُوغَبَنِّنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ نَغِدَجٜىٰنْ كَاكَنِّنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sulemanu ya yi magana da dukan manya, wato shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da alƙalai, da dukan shugabanni na Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanni.