2 Chronicles 10:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce, “Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda, wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse? Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila! Ka lura da gidanka, ya Dawuda!” Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَعَدَّ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا دُكَ سُكَ غَانٜىٰ سَرْكِے بَيْ سَوْرَرٜىٰسُبَ، سَيْ مُتَنٜىٰنْ سُكَ أَمْسَوَ سَرْكِے سُكَثٜىٰ، «إِنَا ضُوَنْمُ دَ دَاوُدَ؟ بَامُ دَ رَبُوانْ غَادُواْ أَوُرِنْ طَنْ يٜىٰسّٜىٰ؞ يَا إِسْرَٰٓءِيلَ، كُواْوَ يَكُواْمَ تٜىٰنْتِنْسَ! بَرِ دَاوُدَ يَلُورَ دَ غِدَنْسَ!» دُواْمِنْ حَكَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ وَڟٜىٰ، كُواْوَ يَكُواْمَ غِدَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Isra'ilawa duka suka ga sarki bai saurare su ba, jama'ar kuwa suka amsa wa sarkin, suka ce, “Wane rabo muke da shi a wurin Dawuda? Ba mu da gādo a wurin ɗan Yesse. Kowa ya tafi alfarwarsa, ya ku Isra'ilawa. Ku bar Rehobowam ya lura da gidansa.” Isra'ilawa duka kowa ya tafi alfarwarsa.