2 Chronicles 10:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki Rehobowam ya aiki Hadoram wanda yake lura da aikin dole, amma Isra’ilawa suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta ya shiga keken yaƙinsa ya gudu zuwa Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً سَرْكِے رٜىٰهُواْبُواْوَمْ يَعَيْكِ أَدُواْنِرَمْ، وَنْدَ يَكٜىٰ شُوغَبَنْ عَيْكِنْ دُواْلٜىٰ ذُوَا وُرِنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا، عَمَّا سُكَ جٜىٰجّٜىٰڢٜىٰشِ دَ دُوَڟُو سُكَ كَشٜىٰ؞ غَنِنْ حَكَ رٜىٰهُواْبُواْوَمْ يَيِ سَوْرِ يَشِغَ كٜىٰكٜىٰنْ دُواْكِ يَغُدُ ذُوَا عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki Rehobowam ya aiki Adoniram shugaban aikin dole, jama'ar Isra'ila kuwa suka jejjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sai sarki Rehobowam ya gaggauta ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima.