2 Chronicles 12:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki Rehobowam ya kafa kansa daram a Urushalima, ya kuma ci gaba a matsayin sarki. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila wanda zai sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama ce, ita mutuniyar Ammon ce.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے رٜىٰهُواْبُواْوَمْ يَكَڢَ مُلْكِنْسَ سُواْسَيْ، يَكُمَيِ ڧَرْڢِے أَ عُرُوشَلِيمَ؞ يَنَ دَ شٜىٰكَرَا أَرْبَعِنْ دَ طَيَ سَعَدَّ يَڢَارَ مُلْكِ؞ يَكُوَ يِشٜىٰكَرَا غُواْمَشَا بَݣَويْ يَنَ مُلْكِ أَ عُرُوشَلِيمَ، بِرْنِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَذَاٻَا دَغَ ثِكِنْ دُكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دُواْمِنْ أَغِرْمَمَ سُونَنْسَ أَوُرِنْ؞ سُونَنْ مَامَرْ رٜىٰهُواْبُواْوَمْ نَعَمَ ثٜىٰ دَغَ ڧَسَرْ أَمُّوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki Rehobowam kuwa ya kafa mulkinsa sosai a Urushalima, yana da shekara arba'in da ɗaya da haihuwa ya ci sarauta, ya yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra'ila domin ya sa sunansa a wurin. Sunan tsohuwar Rehobowam Na'ama, Ba'ammoniya.