2 Chronicles 13:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَنْذُ كُنَ سُواْ كُتُمْٻُكٜىٰ مُلْكٍ دَ يَهْوٜىٰهْ يَكَڢَ وَنْدَ يَكٜىٰ أَ حَنُّنْ یَیَنْ دَاوُدَ؟ عِ، كُنْ غَ كُنَدَ يَوَ، عَمَّا أَلُّواْلِنْكُ سُونٜىٰ غُمَكَنْ صِڢُّواْڢِنْ یَنْ بِجِمَنْ ظِينَارِيَ وَطَنْدَ يٜىٰرُواْبُواْوَمْ يَيِ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun 'ya'yan Dawuda, maza, saboda yawan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku.