2 Chronicles 13:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba ku ne kuka kori firistocin Ubangiji, ’ya’yan Haruna maza, da Lawiyawa kuka kuma zaɓi firistocinku kamar yadda sauran al’ummai suke yi ba? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don yă tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَشٜىٰ، بَكُ كُواْرِ ڢِرِسْتُواْثِنْ يَهْوٜىٰهْ ، ذُرِيَرْ هَٰرُونَ دَ كُمَ سَوْرَنْ لَوِيَاوَا بَ؟ بَكُ نَطَ وَكَنْكُ ڢِرِسْتُواْثِے كَمَرْ يَدَّ ڧَبِيلُنْ وَطَنْسُ ڧَسَاشٜىٰ سُكٜىٰيِبَ؟ دُكْ وَنْدَ يَذُواْ دَ طَنْ بِجِمِ دَ تُمَكِ بَݣَويْ ذَيْ عِيَ ذَمَ ڢِرِسْتِ نَغُمَكَنَّنْ وَطَنْدَ بَ اللَّهْ بَ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ashe, ba ku kori firistocin Ubangiji, 'ya'yan Haruna, maza, da Lawiyawa ba, kuka yi wa kanku firistoci kamar na al'umman sauran ƙasashe? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don ya tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.