2 Chronicles 14:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Abiya kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki, a zamaninsa kuma ƙasar ta zauna lafiya na shekara goma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبِيَ يَكُواْمَ غَ كَاكَنِّنْسَ عَكَ بِنّٜىٰشِ عَبِرْنِنْ دَاوُدَ، وَتُواْ عُرُوشَلِيمَ؞ سَيْ طَنْسَ أَسَ يَغَاجٜىٰشِ يَذَمَ سَرْكِے؞ ڧَسَرْ كُوَ تَسَامِ لَاڢِيَ حَرْ شٜىٰكَرَا غُواْمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki Abaija kuwa ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda. Ɗansa Asa shi ya gāji gadon sarautarsa. Ƙasar ta sami sakewa har shekara goma a zamaninsa.