2 Chronicles 16:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَثٜىٰ «بَرِ مُيِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ دَكَيْ كَمَرْ يَدَّ بَابَنْكَ دَ بَابَنَ سُكَيِ أَدَا؞ غَا ݣَوْتَرْ أَظُرْڢَا دَ ظِينَارِيَ نَعَيْكُواْ مَكَ؞ سَيْ كَوَرْوَارٜىٰ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْكَ دَ سَرْكِے بَعَشَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ دُواْمِنْ يَجَنْيٜىٰ دَغَ ڧَسَاتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Bari mu haɗa kai, da ni da kai kamar yadda ubana da naka suka yi. Ga shi, na aika maka da azurfa da zinariya. Ka tafi ka warware haɗa kan da yake tsakaninka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, don ya janye ya rabu da ni.”