2 Chronicles 17:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗansu Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa a matsayin haraji, Larabawa kuwa suka kawo masa garkuna, raguna dubu bakwai da ɗari bakwai da kuma awaki dubu bakwai da ɗari bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنْسُ دَغَ ثِكِنْ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَ كَٰوُاْ وَ يٜىٰهُواْشَڢَتْ ݣَوْتَرْ كَايَ دَ أَظُرْڢَا دُواْمِنْ هَرَاجِ؞ لَرَبَاوَا سُكَ كَٰوُاْ مَسَ تُمَكِ دُبُو بَݣَويْ دَ طَرِے بَݣَويْ دَ أَوَكِ دُبُو بَݣَويْ دَ طَرِے بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai waɗansu daga cikin Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa domin haraji. Larabawa ma suka kawo masa raguna dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700), da bunsurai dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700).