2 Chronicles 18:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da suka iso, sarki ya tambaye shi, “Mika, mu tafi mu yaƙi Ramot Gileyad, ko kada mu tafi?” Ya amsa, “Kai masa yaƙi za ka kuwa yi nasara, gama za a ba da su a hannunka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يَذُواْ غَبَنْ سَرْكِے أَهَبْ، سَيْ سَرْكِے يَثٜىٰمَسَ «مِكَيَ، مُتَڢِے مُڢَاطَوَ رَمُواتْ غِلٜىٰيَدْ دَ يَاڧِ، كُواْ إِنْبَرِ؟» مِكَيَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «غَسْكِيَ نٜىٰ، ڢَاطَ مُسُ دَ يَاڧِ، أَيْ ذَاكَثِ نَصَرَا، ذَاعَ بَاشٜىٰسُ أَ حَنُّنْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Mikaiya ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu haura zuwa Ramot-gileyad mu fāɗa mata da yaƙi, ko in haƙura?” Mikaiya kuwa ya amsa, ya ce, “Ka haura, gama za ka ci nasara, gama za a bashe su a hannunka.”