2 Chronicles 18:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan ’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ یَنْ شٜىٰكَرُ، سَيْ يٜىٰهُواْشَڢَتْ يَغَنْ‌غَرَ ذُوَا سَمَرِيَ عَ إِسْرَٰٓءِيلَ دُواْمِنْ يَظِيَرْثِ سَرْكِے أَهَبْ؞ سَيْ أَهَبْ يَيِ بِكِ يَيَيَّنْكَ تُمَكِ دَ بِجِمَيْ دَيَوَ دُواْمِنْ يَغِرْمَمَ يٜىٰهُواْشَڢَتْ دَ مُتَنٜىٰنْسَ؞ سَيْ أَهَبْ يَلَلَّشِ يٜىٰهُواْشَڢَتْ يَهَطَكَيْ دَشِ دُواْمِنْ سُكَيْوَ رَمُواتْ غِلٜىٰيَدْ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan 'yan shekaru sai ya kai wa Ahab ziyara a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki masu yawan gaske, da bijimai da yawa, domin Yehoshafat da mutanen da suke tare da shi. Ahab ya rinjaye shi don su fāɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi.