2 Chronicles 18:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa duka, mutane ɗari huɗu, ya kuma tambaye su, “Mu tafi yaƙi a kan Ramot Gileyad ko kada mu tafi?” Suka amsa “Tafi, gama Allah zai ba da shi cikin hannun sarki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے أَهَبْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَتَتَّارَ أَنَّبَاوَا مُتُمْ طَرِے حُطُ يَتَمْبَيٜىٰسُ يَثٜىٰ «مُتَڢِے مُڢَاطَوَ رَمُواتْ غِلٜىٰيَدْ دَ يَاڧِ، كُواْ مُبَرِ؟» سَيْ سُكَ أَمْسَ دُكَنْسُ سُكَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، سَرْكِے! كَتَڢِے، غَمَا اللَّهْ ذَيْبَادَسُو أَ حَنُّنْكَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ahab kuwa ya tattara annabawa, mutum ɗari huɗu, ya ce musu, “Mu je mu faɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi, ko in haƙura?” Sai suka ce, “Ka tafi, gama Allah zai ba da ita a hannun sarki.”