2 Chronicles 18:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, “Akwai guda har yanzu mai suna Mikahiya ɗan Imla, za mu iya nemi nufin Ubangiji daga gare shi, sai dai ba na sonsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai kullum masifa.” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Kada sarki yă faɗa haka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے أَهَبْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «أَݣَويْ وَنْدَ ذَامُ عِيَ نٜىٰمَنْ نُڢِنْ يَهْوٜىٰهْ دَغَ غَرٜىٰشِ، سُونَنْسَ مِكَيَ طَنْ إِمْلَ؞ عَمَّا ڢَا نَڧِ جِنِنْسَ دُواْمِنْ بَايَ أَنَّبْثِ مَيْݣَوْ عَكَيْنَ، سَيْدَيْ مَسِيڢَ؞» يٜىٰهُواْشَڢَتْ يَثٜىٰ «أَعَ، سَرْكِے، كَدَ كَيِ مَغَنَ حَكَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Akwai sauran mutum guda wanda za mu iya neman nufin Ubangiji daga gare shi, shi ne Mikaiya, ɗan Imla, amma na ƙi shi saboda ba ya yin annabcin kirki a kaina, sai dai na rashin alheri kullum.” Amma Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”