2 Chronicles 18:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saye da rigunan sarakuna, sarki Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zaune a kan kujerunsu na mulki a masussuka ta ƙofar shigar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے أَهَبْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ سَرْكِے يٜىٰهُواْشَڢَتْ نَ يَهُودَ سُكَسَا رِيغُنَنْسُ نَسَرَاكُنَ، سُكَ ذَوْنَ عَكَنْ كُجٜىٰرُنْ مُلْكِ كُسَدَ وُرِنْ بُغُنْ حَڟِ نَبَاكِنْ ڧُواْڢَرْ بِرْنِنْ سَمَرِيَ؞ دُكَنْ أَنَّبَاوَنْ ڧَسَرْ سُكَيِ تَأَنَّبْثِ أَغَبَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A sa'an nan Sarkin Isra'ila, da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune kowa a gadon sarautarsa, kowane ya caɓa ado, suna kuwa zaune a filin da yake ƙofar Samariya. Dukan annabawa kuwa suna ta yin annabci a gabansu.