2 Chronicles 19:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَبِرْنِنْ عُرُوشَلِيمَ كُوَ، يٜىٰهُواْشَڢَتْ يَنَطَ وَطَنْسُ لَوِيَاوَا دَ ڢِرِسْتُواْثِے دَ شُوغَبَنِّنْ ذُرِيَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، سُذَمَ مَاسُ شَرِيعَ بِسَغَ كُواْيَرْوَرْ يَهْوٜىٰهْ ، سُكُمَ ذَمَ مَاسُ شِرْيَ ڟَكَانِنْ مُتَنٜىٰ؞ أَ عُرُوشَلِيمَ نٜىٰ ذَاسُ ذَوْنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yehoshafat kuma ya naɗa waɗansu Lawiyawa, da firistoci, da waɗansu shugabannin iyalan Isra'ilawa, saboda su yi shari'a tsakani da Ubangiji, su daidaita tsakanin masu jayayya. A Urushalima za su zauna.