2 Chronicles 2:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya sa 70,000 a cikinsu su zama ’yan ɗauko, 80,000 kuma su zama masu fasan dutse a tuddai, sa’an nan 3,600 su zama shugabanni masu lura da aiki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَسَا دُبُو سَبَعِنْ ثِكِنْسُ سُكَ ذَمَ مَاسُ ݣُوشٜىٰ كَايَ، دُبُو تَمَٰنِنْ كُمَ مَاسُ سَسَّڧَ دُوَڟُو عَتُدَّيْ، سَعَنً دُبُو عُكُ دَ طَرِے شِدَ سُذَمَ مَاسُ لُورَ دَ سَوْرَنْ مَعَيْكَتَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya zaɓi mutum dubu saba'in (70,000) daga cikinsu su zama masu ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) kuma don su riƙa haƙo duwatsu daga tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuwa don su zama shugabanni.