2 Chronicles 2:4 โ Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu ina shirin ginin haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, in kuma keษe shi gare shi don ฦona turare mai ฦanshi a gabansa, don kuma ajiyar burodi mai tsarki kullum, da kuma don miฦa hadayun ฦonawa kowace safiya, kowace yamma, da a Asabbatai da Sababbin Wata, da kuma a ฦayyadaddun bukukkuwan Ubangiji Allahnmu. Wannan dawwammamiyar farilla ce don Israโila.
Hausa Arabic 2020 (ุงููุชููููุฑูุชู ุฏู ุงูููููุจูุงููุง)
ุบูุงุดูุ ุงูููู ุณููุงู ุงูููู ุบูููุง ุบูุฏูุง ุฏููุงูู
ููู ุงููุบูุฑูู
ูู
ู ุณูููููู ููููููููฐูู ุงูููููู ููุงุ ุฐููู ููููฐูปูููฐ ุบูุฏููู ุฏููุงูู
ููู ุนฺูงููุงููู ุชูุฑูุงุฑูููฐ ุงููุบูุจูููุณูุ ุฏููุงูู
ููู ููู
ู ุนู ุงููุฌูููููฐ ุบูุฑูุงุณูุฑู ุฏู ุนููู ููููฐูปูููฐ ูููููู
ูุ ุฏููุงูู
ููู ููู
ู ุงูู ู
ฺููงู ููุฏูุงูู ฺููงููุงูููุงููุง ูููุงูููุซูููฐ ุณูุงฺขููู ุฏู ููู
ูู ุฏู ููุฑูุงูููููู ูููุชู ุชูู
ููููุงู ุฏู ููุจููููููููู ุณูุงุจููุงูู ููุชู ุฏู ููุณูููุฑููู ุจููููููููู ุฏู ููููููููฐูู ุงูููููู ููู
ู ููุนูู
ูุฑูุชูุ ููููููู ฺงููฐุนูุฏู ุซูููฐ ุชูุฏูููุฏูููุฏููู ุฏููุงูู
ููู ุฌูู
ูุนูุฑู ุงููุณูุฑููฐูุกููููุ
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keษe masa shi, domin a riฦa ฦona masa turare mai daษin ฦanshi, inda kuma za a riฦa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riฦa miฦa hadayun ฦonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ฦayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riฦa yi a cikin Isra'ila.