2 Chronicles 2:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma wa zai iya gina haikali dominsa, shi wanda sammai, har ma da sama sammai, ba za su iya riƙe shi ba? To, wane ne ni da zan gina haikali dominsa, in ba dai wurin ƙona hadayu a gabansa ba?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا كُمَ وَ يَ إِسَ يَغِنَ مَسَ غِدَا؟ أَيْ، سَمَ دَ سَمَنْ سَمَّيْ، بَسُ إِشٜىٰشِيبَ! وَنٜىٰنٜىٰنِے حَرْ دَ ذَنْعِيَ غِنَا مَسَ غِدَا؟ أَعَ، سَيْدَيْ كُواْ إِنْ غِنَا غِدَنْ دَ ذَاعَ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ أَغَبَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma wa ya isa ya gina masa Haikali, shi wanda sama da saman sammai ba su iya ɗaukarsa ba. Ni wane ne da zan gina masa Haikali, sai dai wurin da za a riƙa ƙona turare a gabansa?