2 Chronicles 22:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake ’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan ’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَذَوْنَنْ عُرُوشَلِيمَ سُكَ نَطَ أَهَظِيَ، أَوْتَنْ سَرْكِے يٜىٰهُواْرَمْ، يَغَاجٜىٰشِ يَذَمَ سَرْكِنْ يَهُودَ؞ غَمَا ڧُنْغِيَرْ مُتَنٜىٰنْ دَ سُكَذُواْ دَ لَرَبَاوَا سُنْ كَٰوُاْ هَرِ أَ سَنْسَنِنْ يَاڧِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، سُكَ كَكَّشٜىٰ دُكَنْ سَوْرَنْ یَنْعُوَنْ أَهَظِيَ؞ تَهَكَ سَرْكِے أَهَظِيَ يَڢَارَ مُلْكِ أَ يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai mazaunan Urushalima suka naɗa Ahaziya, autansa, ya gāji gadon sarauta, saboda ƙungiyar mutanen da suka zo tare da Larabawa a sansanin sun karkashe dukan 'yan'uwansa maza. Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya fara mulki.