2 Chronicles 22:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya sami fadawan Yahuda da kuma ’ya’yan dangin Ahaziya maza, waɗanda suke yi wa Ahaziya hidima, sai ya kashe su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يٜىٰهُو يَكٜىٰ ثِكَ حُكُنْثِنْ يَهْوٜىٰهْ عَكَنْ غِدَنْ أَهَبْ، سَيْ يَسَدُ دَ شُوغَبَنِّنْ يَهُودَ، تَرٜىٰدَ یَیَنْ یَنْعُوَنْ أَهَظِيَ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ مَسَ حِدِمَ؞ سَيْ يٜىٰهُو يَكَكَّشٜىٰسُ دُكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya gamu da sarakunan Yahuza, da 'ya'yan 'yan'uwan Ahaziya, maza, suna yi wa Ahaziya hidima, sai ya karkashe su.