2 Chronicles 23:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A shekara ta bakwai Yehohiyada ya nuna ƙarfinsa. Ya yi alkawari da shugabanni na ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, Ishmayel ɗan Yehohanan, Azariya ɗan Obed, Ma’asehiya ɗan Adahiya, da Elishafat ɗan Zikri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ شٜىٰكَرَا تَبَݣَويْ سَيْ يٜىٰهُواْيِدَ يَيِ ڧَرْڢِنْ ذُوثِيَا يَطَوْرَا يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ تَرٜىٰدَ شُوغَبَنِّ بِيَرْ نَسُواْجُواْجِ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ شُوغَبَنْثِنْ ڧُنْغِيُواْيِنْ سُواْجُواْجِ طَرِے طَرِے؞ غَا سُونَيٜىٰنْسُ، أَظَرِيَ طَنْ يٜىٰرُواْهَمْ دَ إِسْمَٰعِيلُ طَنْ يٜىٰهُواْهَنَنْ دَ أَظَرِيَ طَنْ عُواْبٜىٰدْ دَ مَعَسٜىٰيَ طَنْ أَدَيَ دَ عٜىٰلِشَڢَتْ طَنْ ظِكِرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya yi ƙarfin hali, ya haɗa kansa da shugabanni na ɗari ɗari, wato Azariya ɗan Yeroham, da Isma'ilu ɗan Yehohanan, da Azariya ɗan Obed, da Ma'aseya ɗan Adaya, da kuma Elishafat ɗan Zikri.